Ba Zan Daina Takarar Shugaban Ƙasa Ba Matuƙar Ina Raye — Atiku

Spread the love

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ce zai ci gaba da neman kujerar shugabancin ƙasar nan, matuƙar yana raye da kuma cikin ƙoshin lafiya.

Atiku ya yi ƙarin haske kan adadin da ya yi takara ba tare da ya yi nasara ba, inda ya ce tsohon shugaban kasar Amurka, Abraham Lincoln sai da ya yi takara sau bakwai kafin ya kai ga nasara.

Atiku, ya bayyana haka ne yayin wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka.

“Tabbas, zan ci gaba da tsayawa takara matuƙar ina da rai da kuma ƙoshin lafiya,” in ji Atiku.

“Ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln sai da ya yi takara sau bakwai kafin daga bisani ya yi nasara.”

Atiku mai shekara 77 a duniya, wanda zai cika shekara 81 a lokacin babban zaɓen 2027, ya yi martani game da rikicin da ke faruwa a jam’iyyar PDP, inda ya tabbatar da cewa dole ne ’ya’yanta jami’yyar su haɗa kai domin samun nasara a gaba.

“Duk da haka, idan aka yi la’akari da halin da jam’iyyar PDP ke ciki a yanzu, a bayyane yake cewa ɓangare ɗaya ba zai kai mu ga cin zaɓe ba. Akwai buƙatar goyon baya daga wasu jam’iyyun,” in ji shi.

A makon da ya gabata ne, Atiku ya ce yana tattaunawa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, a zaben 2023, Peter Obi, kan yiwuwar haɗewa waje ɗaya.

“Ga duk wanda yake tunanin za a samu rashin fahimta tsakanina da Obi, ina tabbatar muku da cewa babu abin da zai faru a tsakaninmu,” in ji Abubakar.

“Kazalika, za mu mara wa duk wanda aka zaɓa ya wakilce mu a zaɓe mai zuwa.

“Na bayyana ƙarara a jawaban da na yi a baya cewa idan jam’iyyunmu za su haɗe su amince da ɗan takara daga yankin kudu maso gabas, matuƙar ya cancanta, za mu mara masa baya.

Atiku, ya ce ya nemi shugabancin Najeriya har sau shida, daga shekarar 1993, 2007, 2011, 2015, 2019 da kuma 2023.

Ya yi takara a zaɓen fidda gwani a jam’iyyar SDP a 1993, amma ya sha kaye a hannun, Moshood Abiola.

Ya yi takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Action Congress a zaɓen 2007, inda ya ƙare a mataki na uku a bayan Umaru Yar’Adua na PDP da Muhammadu Buhari na jam’iyyar ANPP.

Ya sake neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2011, inda ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Goodluck Jonathan.

A 2014, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2015, inda ya faɗi zaɓen fidda gwani a hannun Muhammadu Buhari.

A shekarar 2017, ya koma jam’iyyar PDP, kuma ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2019, inda ya sake shan kaye a hannun shugaban ƙasa mai ci Muhammadu Buhari.

Takarar ƙarshe da Atiku ya yi, ita ce a 2023, inda ya sha kaye a hannun shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *