Ƙwararru a fannin tsaron intanet sun yi gargaɗin cewa za a iya ƙara samun katsewar intanet saboda masu aikata laifi da ke son amfani da yanayin da ake ciki domin cimma burin su.
Yau da safe hukumar kula da tsaron intanet ta Australia ta fitar da wata sanarwar gargaɗi a kan yunƙurin da wasu ke yi domin aikata laifuka da sunan suna aiki ne a kamfanin CrowdStrike.
Sanarwar ta ce “Munafargar da jama’a cewa akwia wasu ɓata gari da ke aikewa mutane adireshin shiga wani shafi, tare da iƙirarin cewa za su gudanar da wasu gayre-gayre ne.
Hukumar ta buƙaci masu huɗɗa da intanet su kiyaye bayanan su da kuma daina shiga adireshin da babu tabbacin sahihancin sa.