Ƙwararrun direbobi ne kawai za su riƙa tuƙa tankokin mai –Minista

Spread the love

Minista a ma’aikatar albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya ce gwamnatin Najeriya ta fara yunƙurin tsara wasu dokoki domin tabbatar da cewa ƙwararrun direbobi ne kawai za su riƙa tuƙa tankokin mai, sannan za a riƙa duba motocin sosai kafin a ba su dama suka riƙa jigilar albarkatun man fetur a ƙasar.

Ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje garin Majia da ke ƙaramar hukumar Taura da ke jihar Jigawa bayan fashewar tankar mai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, “ina ƙara kira ga ƴan Najeriya da cewa duk lokacin da suka ga irin wannan matsalar ta auku, su yi gaggawar sanar da ƴansanda ko wasu jami’an tsaro domin a tsare wurin domin hana mutane zuwa.

“A ɓangaren gwamnati muna ƙoƙarin tsara wasu dokoki domin hana sake aukuwar lamarin. Tun daga tabbatar da ƙwararrun direbobi ne suke jigilar man, sannan dole motoci su kasance suna cikin hayyacinsu,” in ji shi.

“Don haka za mu ɗauki namu matakan a matsayin gwamnati, mutane ma suna da rawar da za su taka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *