Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum 22 a Katsina

Spread the love

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 22 a garin Runka da ke ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce maharan sun afka masu ne tsakar dare lokacin da yawancin jama’a ke barci.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Abdul Jalale Haruna Runka ya ce: ”Abubuwa ne gasu nan babu daɗi, ana ta ƙoƙarin tattarewa amma mu kanmu abin ya ɗaure mana kai saboda duk wani inda muke samun information cewa gasu nan zasu fito, babu wani information da aka samu ba kamar yadda aka saba a baya da ake samun bayanin cewa suna nan tafe. Wannan kawai sai dai aka gansu a tsakiyar gari”

Ya yi bayanin cewa a yanzu sun duƙufa domin nazarin yadda lamarin ya faru da kuma irin matakan da ya dace a ɗauka a kai.

Shugaban ƙaramar hukumar Safana, Abdullaye Sani Safana ya ce yanzu haka suna da tabbacin cewa maharan suna riƙe da mutum 22 ”Da sun fi haka, amma akwai waɗanda suka dawo cikin dare da kuma safiyar Lahadi, a cikin su”

Ya kuma bayyana yaƙinin cewa al’umma za su ci gaba da bayar da haɗin kai da goyon baya domin ganin an ceto waɗanda aka yi garkuwa dasu.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce tuni aka jibge jam’an tsaro domin aikin kwato mutanen da kuma tabbatar da ba a sake samun irin hakan ba a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *