Ƴan majalisa sun gayyaci shugaban jami’ar Dutsin-Ma kan ‘rashin iya shugabanci’

Spread the love

Kwamitin majalisar wakilai da ke kula da korafe-korafen jama’a ta gayyaci shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Armayau Hamisu Bichi da ya bayyana gabanta domin amsa tambayoyi kan zargin ‘rashin iya jagoranci’ da ake yi masa.

Gayyatar tasa ta biyo ne bayan wani mai suna Shehu Abubakar Tadda ya shigar da korafi kan yadda Farfesa Bichi yake tafiyar da salon shugabancinsa wanda bai dace ba, a cewarsa.

Sanarwar ta ce ko da bai bayyana gaban kwamitin ba, za a iya ci gaba da sauraron batun a bayansa.

Majalisar wakilan ta ce gayyatar na a sashe na 88 da kuma 89 na kundin mulkin Najeriya, wanda ya ba ta damar bincike kan batutuwa da suka shafi al’umma.

Haka kuma, majalisar ta buƙaci wanda ya shigar da korafin Shehu Abubakar Tadda da shi ma ya bayyana gabanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *