Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta sake kashe wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne a karamar hukumar Ahoada ta Yamma da ke jihar.
Ana kyautata zaton cewa shugaban ƙungiyar mai suna Ikem Thankgod wanda aka fi sani da General 2man, na da hannu a kisan DSP Bako Angbashim.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta fitar a ranar Litinin, ta ce 2man da yaran gidansa sun yi artabu da ‘yan sandan dabarun yaƙi.
- An Kama Mutum 5 Kan Satar IPhone 13 Yayin Sallar Tahajjud A Abuja
- Ba a ga watan sallah a Najeriya ba
Ƴan sandan sun ce Thankgod ya salwantar da rayukan mutane da dama a jihar, inda ya kuma binne mutane da dama da ransu a watan da ya gabata.
“Ya yi garkuwa da mutane da dama a ciki da wajen karamar hukumar Ahoada ta Yamma. Yana fashi da makami da lalata kayyaki,” in ji sanarwar ƴan sandan.
Sun kuma ce ya ɗauki kansa a matsayin hukuma, abin da ya sa ma yake far wa wuraren bukukuwan aure da kuma taron bizina da sauransu.