Rundunar ƴan sanda a Kano ta ce ta kama mutum 149 saboda zarginsu da ayyukan fashi da makami da daba da garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka cikin kwanaki 10 da suka gabata.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka a lokacin da yake magana da manema labarai game da kamen da rundunar ta yi.
Ya ce an kama ƴan daba 106 da waɗanda ake zargi masu fashi da makami ne su 25 da mutum biyu da ake zargi suna garkuwa da mutane sai masu satar mota uku da dillalan miyagun ƙwayoyi uku a sassa daban-daban na jihar.
“Mun kuma gano motoci biyu da babura takwas da wuƙaƙe 58 da bindiga ɗaya da ƙunshi 87 na abin da ake zargin tabar wiwi ne.
Kiyawa ya ce kamen ya biyo bayan shawagin da ƴan sanda suke yi a sassan jihar domin hana aikata laifuka.
- Binciken Ganduje: Kotu Ta Ba Shugabannin Kwamiti Awa 48 Su Sauka
- Kwastam Sun Kama Makaman N1.6bn A Filin Jirgin Legas
A cewarsa, mutanen da aka kama na sashen binciken manyan laifuka na rundunar inda ake gudanar da bincike a kan su.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Salman Dogo Garba ya ce rundunar za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.