Ƴan sandan sun kama waɗanda ake zargin sun shirya zanga-zanga a Neja

Spread the love

Rudunar ƴansandan Najeriya a jihar Neja ta tabbatar da kama wata mata mai shekaru 30 da ake zargin ita ce ta jagoranci mata da matasa domin gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a garin Minna na jihar a ranar Litinin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sanda a jihar ta Neja DSP Abiodun Wasiu ya fitar ya ce sun kama Matar ne tare da wasu mata biyu masu shekaru 57 da 43, da karin wasu mutum 22.

Wata kungiya a Kano ta bukaci a rusa masarautu, a mayar da Khalifa Sanusi

Sanarwar mai magana da yawun yan sandan na Neja DSP Abiodun Wasiu ta ce sun kama mutanen ne sakamakon yadda masu zanga-zangar suka tayar da rikici a lokacin gudanar da ita.

Matasa maza da mata a Neja ne dai suka fito kan titunan babban birnin jihar a ranar Litinin, domin kokawa kan abun da suka kira halin matsi da tashin farashin kayan masarufi a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *