Rundunar ƴansanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta kama wani jami’in gidan gyaran hali da ake zargi da harbe wani mutum mai suna Ibrahim Yahaya a kasuwar Wuse da ke tsakiyar birnin.
Kisan mutumin dai ya janyo hatsaniya a kasuwar da yammacin ranar Talata, lamarin da ya janwo asarar dukiya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴansanda a Abuja, Josephine Adeh ta turo wa BBC, ta ce jami’in ya harbe Yahaya ne a lokacin da yake yunƙurin tserewa bayan da rundunar tsaftace Abuja ta Taskforce ta kama shi ta kuma gurfanar da shi a gaban wata kotun tafi da gidanka da ke Kasuwar Wuse, inda aka yanke masa hukunci.
Sanarwar ta ƙara da cewa yanzu haka rundunar tana tsare da jami’in inda take gudanar da bincike.
Hukumar Hisbah A Kano Ta Cafke Gandaye 12.
sun sake sace mutum 61 a Kaduna