Ɓangaren marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya nemi a hukunta wasu alƙalai

Spread the love

Bangaren marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya yi kira da a sanya takunkumai a kan wasu alkalan kotun daukaka karan kasar, wadanda ke da alhakin cire ‘yan majalisar jihar Filato.

Dan majalisa Chinda Kingsley, shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.

Inda ya jaddada cewa ya kamata a daure alkalan da suka yi shari’ar don ya zamo darasi ga sauran alkalan masu irin wannan tunani a nan gaba.

A watan Nuwambar 2023 ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kori baki-daya ‘yan majalisar dokoki jihar ta Filato16, na jam’iyyar PDP.

Kotun ta kore su ne saboda wasu dalilan da suka shafi matsaloli kafin zabe, zargin kin biyayya ga kotu da kuma rashin iya gudanar da mulki.

Kafin sannan, kotun daukaka karar ta cire wasu ‘yan majalisar wakilai daga jam’iyyar PDP su hudu da kuma sanatoci biyu.

Kingsley ya kuma taya ‘yan jam’iyyar adawar da suka samu nasara a kotun kolin kasar murna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *