Ɗana ya cancanci zama kwamishina – Oshiomhole

Spread the love

Sanata mai wakiltar mazaɓar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce ɗansa, Cyril, ya cancanta kuma yana da ƙwarewar da ta dace domin zama kwamishinan lafiya a jihar Edo.

Sanata Oshiomhole, wanda tsohon gwamnan jihar ne yana tsokaci ne game da martanin da ya biyo bayan naɗin da gwamnan Edo Monday Okphebolo ya yi wa Cyril Oshiomhole a matsayin kwamishinan lafiya a cikin watan Nuwamba.

Naɗin nasa dai ya janyo ƙorafi daga jama’a, masu ganin cewa kamar gwamnan ya saka wa Sanata Oshiomhole ne saboda gudunmuwarsa a zaɓen gwamnan.

Amma a wata hira da gidan talabijin na Channels a Najeriya, Sanata Oshiomhole ya ce tun da daɗewa ɗan nasa ya cancanta riƙe muƙami a jihar, inda ya nemi takarar majalisar wakilai, amma mahaifin nasa ya hana shi saboda a lokacin shi ne gwamna.

Ya yi bayanin cewa a yanzu lokaci ya yi da zai bari ɗan nasa ya shiga a dama da shi domin bayar da gudunmuwa wajen ciyar da jihar ta Edo gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *