Ƙaruwar fursunoni ma su dakon shari’a na janyo cunkoso a gidajen yarin Kano

Spread the love

Hukumar da ke lura da gidajen gyaran hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta nuna damuwa kan ƙaruwar masu zaman jiran shari’a a gidajen yari da ke faɗin jihar.

Wata sanarwa da kakakin hukumar reshen jihar Musbahu Lawan ya fitar, ta ce ƙaruwar mutanen da ke jiran a yanke masu hukunci na kawo wa hukumar cikas wajen gudanar da ayyukanta a jihar, inda ya ce yawan fursunoni masu jiran shari’a ya ninƙa har sau uku idan aka kwatanta da waɗanda aka yanke wa hukunci a jihar.

“Fursunoni ma su zaman shari’a ya kai kashi 70 na ɗaukacin fursunoni da ake da su a faɗin jihar, ana tsare da yawancinsu duk da cewa kotu ba ta kammala yanke hukunci kan shari’o’insu ba,” in ji Musbahu.

Kofar Nasarawa ya ce idan da a ce an yanke wa mutanen da ke zaman jiran shari’a hukunci, to da hukumar ba za ta yi ƙorafi kan cikar gidajen yarin ba, saboda doka ta ba su damar sauya wa fursunonin da aka yanke wa hukunci wurin zama zuwa ko’ina a faɗin ƙasar.

Ya ƙara da cewa an fi samun sauƙin kula da fursunonin da aka yanke wa hukunci saboda ana saka su cikin shirye-shiryen gyaran hali, wani abu da waɗanda ke zaman jiran shari’a ba su da damar morar sa.

Mai magana da yawun gidajen gyaran halin, ya ce wasu fursunoni 38 waɗanda aka yanke wa hukunci sun zana jarrabawar kammala sakandare ta NECO, kuma suna neman gurbin karatu a Jami’ar karatu daga gida (NOUN).

Musbahu ya ce duba da ƙaruwar fursunonin da suka nuna sha’awar karatu, hukumar na aiki da Jami’ar ta NOUN domin kafa ƙarin cibiyoyin karatu a gidajen yari a faɗin jihar.

Ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa ɓullo da matakai na yi wa fursunoni afuwa domin shawo kan matsalar cunkoso a gidan gyaran hali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *