Abuja, Najeriya — Halin da Najeriya ke ciki na tattalin arziki ya kai wani mummunan mataki da ke shafar kowa da kowa. Talakawa, ’yan kasuwa, masu albashi, manoma, matasa, ma’aikatan gwamnati da wadanda ba su da aiki — kowa yana kuka da tsananin rayuwa da tsadar abubuwan more rayuwa.
Farashin kaya da ayyuka sun tashi ba kakkautawa, yayin da albashi da kudaden shiga na yawancin ’yan ƙasa ba su canza ba. Hakan ya haifar da matsin rayuwa, yunwa, rashin lafiya, da hauhawar fargaba a tsakanin al’ummah.
- Ana Zargin Ma’aikacin NRC Da Satar Waya.
- Zafin Kishi Ya Sanya Wata Mata Kashe Jariri Da Guba A Kaduna
Muna kiran gaggawa ga Gwamnatin Tarayya, Majalisar Dattawa da Ta Wakilai, Ministoci, da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan jinƙai da sauƙin rayuwa. A rage harajin VAT da sauran haraji da kudade da ke sa kaya su yi tsada. A sake nazarin farashin mai, wutar lantarki da sauran muhimman kayayyaki domin talakawa su iya rayuwa cikin mutunci.
Wannan kiran ya shafi duk wani mai kishin kasa — domin adalci da jinƙai su tabbata a Najeriya. Rayuwar ɗan adam na da daraja, kuma lokaci ya yi da gwamnati za ta kare wannan daraja ta hanyar rage nauyin rayuwa.
Wanda Ya Sanya Hannu:
Amb. Abdullahi Bakoji Adamu
Daraktan Ƙungiyar Kare Hakkin bil Adama Ta Ƙasa Ƙasa IHRC-RFT Reshen Najeriya
23 ga Mayu, 2025