Ƙasashen Afirka biyar masu ƙarfin tattalin arziƙi da al’ummarsu ke wahala

Spread the love

Wani rahoton Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya ce an samu sabon jadawalin ƙasashen da suka fi girman tattalin arziƙi a Afirka.

Najeriya wadda ta taɓa zama ƙasar da tafi kowacce girman tattalin arziki a Afirka yanzu ta sulmiyo zuwa ta huɗu, inda ita kuma ƙasar Afirka ta kudu take saman jadawalin na 2024.

To sai dai girman tattalin arzikin ƙasashen ba wai na nuni da irin rayuwar da mafi yawancin mutanen ƙasashen ke yi ba ne.

Ƙasashe da dama na ci gaba da fuskantar yawaitar basuka da ƙalubalen kayan more rayuwa da hauhawar farashi da kuma koma-bayan tattalin arziki.

Asusun Lamunun na Duniya ya ce matsalolin da tattalin arziki na duniya ke fuskanta da suka haɗa da hauhawar farashi da yawaitar cin bashi da kuma matsalar rashin tabbas na gwamnatoci na matuƙar shafar tattalin arziƙin ƙasashen Afirka.

Ƙasar Afirka ta kudu ita ce ta farko a fannin tattalin arziki sai kuma ƙasar Egypt da ke biye mata. Algeria mai ɗimbin albarkatun man fetur ce ta uku, inda Najeriya wadda ta taɓa kasancewa giwar Afirka yanzu ta zama ta huɗu. Ƙasar Ethiopia ce ta biyar.

“Wannan sabon jadawalin ƙasashen na nuni da irin yadda ƙasashen suka aiwatar da tsare-tsare domin tunkarar ƙalubalen harkokin kuɗaɗe,” In ji Dakta Zainab Usman, darakta a cibiyar Carnegie Endowment for International Peace.

Ta ce ƙasashe kamar su Najeriya da Egypt na fuskantar koma-baya wajen samun kuɗaɗen shiga daga ƙerawa da fitar da kaya, yawan basuka da hauhawar farashi da kuma faɗuwar darajar kuɗaɗen ƙasashen.

“Waɗannan ƙalubalai da tsare-tsaren da suka aiwatar wajen cimma daidaiton farashi ta hanyar rage darajar kuɗaɗensu da ƙara kuɗin ruwa da bankunan ƙasashensu suka yi – sun rage wa ƴan ƙasar ƙarfin iya sayen abubuwa.”

To amma al’amarin bai yi munin da ake gani ba. IMF ya ce Afirka za ta zama nahiyar da tattalin arziƙinta ya fi saurin samun tagomashi, inda tattalin arzikin zai ƙaru da kaso 3.5 a 2024, sannan zai ƙaru da kaso huɗu a 2025.

Ta haka ne IMF yake fasalta tsarin girman tattalin arzikin ƙasashen ta hanyar ƙarfin da suke da shi na ƙudin da ke shigar musu da ake kira GDP, wani mizani da ake amfani da shi na ƙarfin tattalin arzikin ƙasashe, da kamfanoni da kuma al’ummar ƙasa.

Afirka ta Kudu

Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya ce Afirka ta Kudu ta yi zarra a shekarar 2024 inda take da yawan ƙarfin tattalin arikin da ya kai dala biliyan 373.

Ƙasar wadda ta zama wadda ta fi kowacce samar da kaya daga masana’antu ta rungumi tsarin faɗaɗa tattalin arzikinta da suka haɗa da ƙere-ƙere da tonon ma’adanai da noma da kiwo da kuma yawon buɗe ido.

To sai dai duk da kasancewarta ta farko, har yanzu rayuwar mafi yawan ƴan Afirka ta Kudu ta munana.

Binciken ya gano cewa Afirka ta Kudu na kashe fiye da kaso 80 na samunsu a kan al’amuransu na yau da kullum kamar sufuri da abinci da kuɗin haya da wutar lantarki.

Bugu da ƙari, ƙasar na ci gaba da ƙarancin wutar lantarki duk da ƙaddamar da tsarin samar da makamashi da aka yi a watan Agusta, da manufar inganta wutar lantarki.

Hukumar sauyin yanayi ta shugaban ƙasa ta Afirka ta Kudu ta soki tsarin inda ta bayyana shi da wanda bai wadata ba wajen magance matsalar ƙarancin wutar da ya ci karo da tsare-tsaren ƙasashen duniya kan sauyin yanayi.

Masar

IMF ya ayyana Masar a matsayin ƙasa ta biyu mai ƙarfin tattalin arziki, inda take da ƙarfin tattalin arzikin da ya kai na dala biliyan 347.

Ƙasar ta ɗaɗe tana fama da matsalar ƙarancin kuɗaɗen ƙasashen waje da kuma hauhawar farashin kaya.

Farashin abinci ya ƙaru da kaso 45 a watan Maris. Gwamnati ta kuma ƙara kuɗin man fetur, a wani mataki na ƙara ta’azzarar hauhawar farashi wanda ya ƙara rage ƙarfin sayen abubuwa da ƴan ƙasar suke da shi.

A ƴan watanni da suka gabata, Egypt tana da fama da matsalolin yaƙin Isra’ila da Gaza wanda ya rage yawan zirga-zirgar jirage a mashigar Suez Canal, wata babbar hanyar samun kuɗin shigar ƙasar.

Ƙasar dai ta kuma rattaɓa hannu kan wani bashi da ta ciyo daga IMF na dala biliyan takwas, wanda ƙari ne kan rancen farko na dala biliyan uku.

Algeria

IMF ya ce Algeria na da ƙarfin tattalin arzikin da ya kai dala biliyan 267.

An gano ƙasar na cike da ɗimbin albarkatun ƙasa saboda iskar gas, bayan da Rasha ta fara mamaye a ƙasar Ukraine.

Wannan ya ƙara mata yawan kuɗaɗen shiga da kuma inganta tattalin arzikin. To sai dai duk da haɓakar tattalin arziki, hauhawar farashin kaya na ci gaba da ƙaruwa.

Ƙarfin da jama’ar ƙasar ke da shi na sayen abubuwa ya samu tawaya sakamakon ƙoƙarin samar da daidaito tsakanin kawo ƙarshen tsadar rayuwa da ci gaba da biyan tallafi da kuma daidaita hauhawar farashi domin tabbatar da ƴan ƙasa na cikin wadata.

Nigeria

Najeriya ce ta huɗu da yawan tattalin arzikin da ya kai dala biliyan 253, kamar yadda IMF ya ce.

Gwamnatin Najeriya da shugaba, Bola Ahmed Tinubu yake jagora ta ɗauki wasu matakai masu tsauri waɗanda wani ɓangare ne na gyaran fuska ga tattalin arzikin ƙasar da kuma Najeriyar ke cewa su ne dalilin halin matsin da suke ciki.

Ƴan Najeriyar dai sun kwashe shekaru suna fama da matsalar ƙarancin man fetur. Mista Tinubu wanda ya karɓ jagorancin ƙasar a watan mayun 2023, ya soke tallafin mai yana mai cewa tallafin na zuƙe kuɗin ƙasar da ake buƙata wajen raya ƙasa da ilimi da sha’anin lafiya.

Ƴan Najeriya dai yanzu haka na kashe kuɗi masu yawa wajen sayen mai a gidajen mai wani abu da ke wahalar da ƴan ƙasar ta fuskar sufuri da farashin makamashi.

Shugaba Tinubu ya kuma ƙayyade farashin naira maimakon ƙyale nairar ta nema wa kanta daraja a kasuwa. Wani abu da ya fi girgiza ƴan ƙasar shi ne rasa kaso 70 da nairar ta yi na darajarta idan aka kwatanta da dalar Amurka.

“Faɗuwar tattalin arzikin ƙasar ba zai rasa nasaba da yadda aka ƙimanta darajar nairar ba a tsawon shekaru masu dama da kaso 50%, ta yadda ƙimar dala ta yi mata fintinkau,” in ji Charlier Robertson, shugaban kamfanin Macro Strategy.

Hakan na nufin farashin kayan da ake shigar da su ƙasar ya ƙaru tun bayan da ƙasar ta dogara kacokan kan abin da aka shigar da shi domin buƙatun yau da kullum na ƴan ƙasar.

Ethiopia

Ƙasar Ethiopia ce ta biyar a jadawalin ƙarfin tattalin arzikin bisa la’akari da tattalin arziki mai yawan dala biliyan 205, kamar yadda IMF ya ce.

A watan Disamba, Ethiopia ta shiga yanayin da bashi ya mata kakatutu bayan da gwamnatin ƙasar ta gaza biyan dala miliyan 33 na bashin dala biliyan ɗaya da ta ci daga Turai da IMF. Ethiopia dai tana tattaunawa da IMF kan wani tallafin yi wa tattalin arziƙinta garambawul.

Ethiopia wadda ta jikkata daga yaƙin Tigray da ta yi fama da shi na shekara biyu da kuma ƙarancin kuɗin ƙasar da hauhawar farashi da kuma yadda rayuwar ƴan ƙasar ke fuskantar ƙalubale.

Duk da dai alƙaluma daga babban bankin na Ethiopa da ke nuna hauhawar farashi ya faɗo da kaso 23.3 a watan Afrilu idan aka kwatanta da kaso 33.5 a daidai lokacin a bara, kayan abinci kamar hatsi na neman gagarar masu saye.

Ethiopia na cin moriyar tsarin ɗage harajin kaya a kasuwannin Amurka a ƙarƙashin dokarn Haɓaka Tattalin Arzikin Afirka da Damammaki, AGOA.

To sai dai wannan damar ta kuɓuce a watan Disamban shekarar 2021 sakamakon rikicin Tigray. Kuma tun bayan nan kusan kamfanoni 450 ne suka tsaya da aiki kamar yadda wani bincike na hukumar Haɓaka tattalin arziki ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP survey, a daidai lokacin da wasu ke aiki da kaso 30 na yadda ya kamata su yi aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *