Ƙasashen Afirka sun kare matakin aika ɗumbin wakilai zuwa taron Cop28.

Spread the love

Gwamnatocin Afirka da dama sun kare matakinsu na aika yawan wakilai zuwa taron ƙoli kan sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya da ake yi a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, lamarin da ke ci gaba da yamutsa hazo.

Najeriya da Morocco da Kenya da Tanzania da Ghana da Uganda na daga cikin kasashen da suka fi tura wakilai masu ɗumbin yawa a taron.

Najeriya ta aike wakilai 1,411 sai Morocco da 823 sai kuma Kenya da 765.

Wakilan Najeriya da Kenya sun ce galibin wakilan da suka fito daga ƙasashensu, ba gwamnati ce ta ɗauki nauyinsu ba saboda wasun su ƴan jarida ne, wasu kuma ƴan ƙungiyar farar hula da kamfanoni masu zaman kansu.

Ƙasashen biyu sun ce wasu daga cikin wakilan za su halarci taron ne ta intanet.

“A matsayinta na ƙasa mafi girma a Afirka kuma mafi ƙarfin tattalin arziki sannan wadda take da ruwa da tsaki kan sauyin yanayi kasancewarta ƙasar da tattalin arzikinta ya dogara kan harkokin haƙon ma’adanai, ba abin mamaki bane idan yawan wakilan Najeriya suka fi na sauran ƙasashen Afirka,” in ji wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi.

Kakakin Fadar Shugaban Kenya, Husein Mohammed ya faɗa wa gidan Talbijin na Citizen TV cewa an zuzuta adadin wanda ya ƙunshi waɗanda suka yi rajista ba wai waɗanda suka halarta ba.

Al’umomin Nijar Na Maraba Da Matakin ECOWAS Na Janye Wasu Takunkumai

Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar ta ɗauki nauyin wakilai 51 ne, sauran kuma wasu kungiyoyi ne suka ɗauki nauyinsu.

Cikin sanarwar, gwamnatin Tanzania ta ce fiye da kashi 90 cikin 100 na wakilai daga ƙasar, ba gwamnati ce ta ɗaki nauyinsu ba.

Wannan batu dai ya janyo zazzafar muhawara tsakanin al’umomin ƙasashen musamman a shafukan sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *