Ƙungiyar Houthi mai samun goyon bayan ƙasar Iran ta gargaɗi Isra’ila cewa a shirye take ta afka wa Isra’ilar idan har ta koma kai hare-hare a Gaza.
Shugaban ƙungiyar ta Houthi, Abdul Malik al-Houthi ne ya yi kalaman na gargaɗi ne a wani jawabi da ya yi a gidan talbijin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Tundai bayan da yaƙin Gaza ya fara, ƙungiyar ta Houthi da ke Yemen sun ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami duk da cewa Isra’ila ta yi iƙrarin kama wasu.
Ƴan ƙungiyar ta Houthi sun kai hare-hare kan jiragen ruwa a tekun maliya da mashigar Aden da suka ce suna yi ne domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinawa.