Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya na son a binciki lauyoyin Sanusi da Aminu Ado

Spread the love

Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya Nigerian Bar Association (NBA) ya ce ayyukan wasu lauyoyi da ya jawo ba da umarni masu karo da juna daga kotuna kan rikicin masarautar Kano “ya jawo ƙasƙanci” ga ayyukansu.

Yakubu Chonoko Maikyau ya ce “za a ɗauki tsawon lokaci kafin a manta da irin wannan abin kunyar da lauyoyin suka jawo”.

Tun da farko wata babbar kotun tarayya ta nemi a dakata da sauke Sarki Aminu Ado ko sauya dokar masarautun Kano har sai ta kammala sauraron ƙorafin da aka kai mata. Daga baya kuma wata babbar kotun Kano ta ba da umarnin kare Sarki Muhammadu Sanusi II kuma ta yi gargaɗin kada a fitar da shi daga gidan sarauta.

Bugu da ƙari, babbar kotun ta Kano ta sake ba da umarnin bai wa Aminu Ado kariya da kuma gargaɗin kada a fitar da shi daga gidan sarauta.

Sanusi na zaman fada a fadar Gidan Rumfa, yayin da Aminu ke nasa zaman a gidan sarki na Nassarawa.

“Wannan abin takaici ne wanda kuma bai kamata ya faru ba tun farko,” in ji shugaban NBA.

“Saboda haka NBA na kira ga shugabannin kotunan da abin ya shafa su ɗauki matakin gaggawa don gano ko lauyoyin ɓangarorin biyu sun aikata ba daidai ba kuma su aika wa hukumar kula da harkokin shari’a ta ƙasa rahoto don ɗaukar mataki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *