Ƙungiyar sanatocin jihohin Arewacin Najeriya ta ce za ta tura wakilanta jamhuriyyar Nijar, domin ganawa da shugabannin mulkin sojin ƙasar, kan yadda za a mayar da mulki ga farar hula.
Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne, bayan sanar da janye takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙabawa Nijar da Mali da kuma Burkina Faso waɗanda sojoji ke jan ragamar mulkin su.
Kakakin ƙungiyar sanatocin, Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce ƙungiyar zata tura tawagar ba tare da ɓata lokaci ba.
Hedikwatar tsaro ta yi watsi da jita-jitar juyin mulki a Najeriya
Najeriya Ta Maida Wa Nijar Wutar Lantarki
Janye takunkuman da ECOWAS ta yi zai sake buɗe harkokin cinikayya da zai taimaka wajen warware matsalar ƙarancin abinci da magunguna da sauƙaƙa al’amura ga ƙasashen na Najeriya da Nijar da ke makwabtaka da juna.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wata ƙungiyar malaman mususlunci ta Najeriyar ta yi kira da sojoji a Nijar da Mali da Burkina Faso da su koma cikin ƙungiyar ta ECOWAS.