Ƴadda wani magidanci ya kashe matarsa kan ta dauki wayarsa a Adamawa

Spread the love

Rundunar yan sanda a jihar Adamawa ta ce ta kama wani mahauci mai shekara 33, mai suna Ibrahim Abubakar, mazaunin karamar hukumar Girei, da zargin kashe matarsa yar shekara 25, mai suna Hajara Sa’adu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahya Nguroje ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Nguroje ya ce bayan samun korafi daga wajen mahaifin marigayiyar ce kan abin da ya faru, nan take suka kama mijin nata.

Nguroje ya ce wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin da ake zarginsa da shi, kuma ya ce ya kashe matar tasa ne bayan daukar wayarsa da ta yi.

“An same ta kwance cikin jini, sai aka tafi da ita zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta,” in ji Nguroje.

Ya kara da cewa suna ci gaba da gudanar da bincike da kuma tattara hujjoji, kafin gurfanar da shi gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *