Ƴan adawa na neman gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan ɗumbin wakilan da ta tura taro Dubai

Spread the love

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce dangane da ɗumbin wakilan Najeriya har 1,400 da gwamnatin Tinubu ta tura babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP28.

Lamarin dai ya janyo jam’iyyar ƴan adawa ta PDP da na Labour fara gudanar da bincike inda suka buƙaci gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan wanda ya ɗauki nauyin tawagar Najeriya zuwa taron.

Tun bayan da adadin wakilan kasar ya bayyana, masu suka da jam’iyyun adawa suka yi Allah-wadai da shi, suna masu bayyana rashin jin dadinsu idan aka yi la’akari da yanayin tattalin arzikin kasar.

A cewar PDP, wakilan sun yi yawa matuka inda suka hadar da ƴan baranda da matansu da kuma sauran ƴan ku ci ku ba mu da ke da alaƙa da fadar shugaban ƙasar.

“Jam’iyyar mu tana kalubalantar fadar shugaban kasa da ta bayyana sunayen wakilan jami’an da Gwamnatin Tarayya ta dauki nauyin gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na Cop28, da yadda irin wadannan mutane ke da alaka da taron, da kuma kudaden da aka kashe wajen daukar nauyin wannan taro ga al’umma.”

“Tabbas ‘yan Najeriya na da jerin sunayen wakilan kuma sun san jami’an kananan hukumomi da sauran kungiyoyi masu cin gashin kansu da ya kamata su halarci taron,” in ji PDP a wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi.

Rundunar yan sandan Kano ta shirya tsaf don bayar da cikakken tsaro a ziyarar Uwar gidan shugaban kasa Oluremi Tinubu.

Na kamu da cutar tsananin damuwa bayan rabuwa da matata :Zango

‘Yan Najeriya sun cancanci sanin wanda ya bai wa wakilan kasar kudin zuwa taron, kamar yadda kakakin yakin neman zaben jam’iyyar adawa na Labour Party, Yunusa Tanko ya bayyana.

“Abin da muke cewa shi ne lambar wakilan da gwamnati ta dauki nauyi zuwa babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP28 ya kamata a bayyana wa jama’a don mu sani,” in ji shi ranar Litinin kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na Channels.

“Idan gwamnati na cewa ba ta dauki nauyin daukacin wakilai 1,411 ba, to su ba mu lambar wakilan da gwamnati ta dauki nauyinsu.” In ji Tanko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *