Ƴan huɗu na farko da aka haifa a wani gari na Scotland

Spread the love

Wata mata da haifi ƴan huɗu ta bayyana farin cikinta.

Arlene da John Mitchell, da ke Longridge Yammacin Lothian sun zama iyaye ga Ben da Noah da Harrison da Rosy a ranar 14 ga watan Mayu.

Ƙaramin cikinsu, Horrison na da nauyin 2lb 14oz, yayin da Ben da Noah da Rory kowannensu na da nauyin 2lb 15oz

Arlene ta ce ta yi matuƙar farin ciki da haihuwar ƴan hudu.

Ba’a cika samun ƴan huɗu ba, inda likitoci suka ce aƙalla ana samun guda a duk cikin haihuwa 700,000.

Su ne ƴan hudu na farko da aka fara haifa a Lothian.

Arlene ƴar shekara 34 da mijinta mai shekara 38 na da ƴa ƴar shekara 11 mai suna Lauren da kuma ɗa namiji mai shekara uku, Hunter.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *