Ƴan kasuwar Kantin kwari sun yi addu’a kan matsin rayuwa a Najeriya

Spread the love

Wasu ƴan kasuwa da ke hada-hada a kasuwar Kantin kwari da ke birnin Kano sun gudanar da addu’o’in neman samun sauƙi kan matsin tattalin arziƙi da ake ciki a Najeriya.

Ƴan kasuwar sun fito daga kantunansu inda suka gudanar da sallah da addu’o’i tare da neman ɗauki daga ubangiji.

Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar mai suna Hamisu Sani ya shaida wa BBC cewa al’amura sun rincaɓe inda yanzu haka abinci ke gagarar al’umma.

Ya ce “mun gudanar da addu’o’i domin samun ɗauki daga ubangiji kan wannan hali, domin ba mu san abin da shugabanni ke yi kan wannan hali ba.”

Hukumar ilimin bai daya ta jahar Kano za ta hukunta malaman makarantar da basa zuwa wajen aiki: Malam Yusuf Kabir

Kano: Kotu ta bayar da belin Danbilki Kwamanda

Ya ƙara da cewa “Buhun shinkafa da na sukari a yanzu haka sun gagari talaka.”

Tashin kayan masarufi ya munana a Najeriya cikin kwanakin nan.

Lamarin ya ƙazance ne sanadiyyar wasu daga cikin shirye-shiryen da gwamnati ta ɓullo da su, kamar na cire tallafin man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *