Ƴan sanda na bincike kan bidiyon cin zalin ɗalibar jami’ar jihar Ekiti

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta ce ba ta da masaniya kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna yadda wata dalibar jami’ar ilimi da kimiya da fasaha ta Bamidele Olumilua, Ikere take cin zalin wata ɗaliba ƴar uwarta a wani wuri mai kama da daji.

Rundunar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.

“Wannan sanarwar na son sanar da ƴan Najeriya da kuma mutanen jihar EkitI cewa rundunar ‘yan sandan jihar ba ta da masaniya kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna wata ɗalibar jami’ar jihar, BOUESTI tana cin zalin ɗaliba ƴar uwarta.” in ji sanarwar.

“Rundunar ta bayyana irin wannan cin zalin a matsayin rashin mutuntaka kuma ba za a yarda da shi ba.”

Rundunar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Ekiti, CP Akinwale Kunle Adeniran ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin domin tuni ya umurci kwamandan yankin Ikere da ya haɗa kai da hukumar gudanarwar jami’ar tare da tabbatar da an gano wadda ta aikata wannan laifin don fuskantar sakamakon shari’a.

Sanarwar ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu kuma su guji daukar doka a hannunsu domin ana daukar matakan da suka dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *