Ƴan sanda na neman ɗan Birtaniya ruwa a jallo kan yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu

Spread the love

Rundunar ƴansanda Najeriya ta ayyana neman wani ɗan Birtaniya, Andrew Wynne, wanda ake kira Andrew Povich da wani ɗan Najeriya mai suna Lucky Obiyan bisa zargin su da yunƙurin kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnati a ƙasar.

Ƴansanda sun zargi ɗan Birtaniyar da haɗa kan wasu mutane domin ƙulla yadda za a bi a kifar da gwamnati, sannan a jefa ƙasar a ciki ruɗani.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya ce Wynne ya kama haya a ginin da ake kira ‘Labour House’ da ke Abuja, sannan ya buɗe makaranta domin ya ɓatar da kama.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Ya ce, “Rundunar ƴansan Najeriya ta ƙaddamar da bincike mai zurfi a kan ayyukan baƙin hauren da waɗanda ya haɗa baki da su domin kifar da gwamnatin da ƴan Najeriya suka zaɓa tare da haifar da ruɗani a kasar.

“Bayan bin diddigi da tattara wasu bayanan sirri tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro, mun kama mutum tara waɗanda suke samun tallafin kuɗaɗe daga ƙasashen waje domin jawo ruɗu a ƙasar.

“Binciken farko ya nuna cewa sun ɗauki nauyin zanga-zanga, sun kuma yaɗa labaran ƙarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *