Ƴan sanda na neman waɗanda suka yi wa wani yaro mummunan kisan gilla a Zariya

Spread the love

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da gano gawar wani yaro ɗan shekara takwas, wandaaka ba da rahotonsa ɓatansa a baya-bayan nan lokacin da suka je ziyara unguwar Kwanar Ɗangoma a cikin birnin Zaria.

Rundunar yan sandan jahar Kano ta cafke masu satar kananan yara su 9 – Idongari.ng

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Mansur Hassan ya ce an kira jami’ansu ne bayan ganin gawar yaron a yashe kuma sun ga jini a kafofin jikinsa kamar idanu da dubura da sauran sassa.

Za mu ci gaba da sayar da sumunti 3,500 – BUA – Idongari.ng

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

A ranar Laraba ne, aka fara ganin cigiyar Ibrahim Muntaqa Mohammed, wanda wasu ke cewa yana da lalura irin ta ƙwaƙwalwa da ake kira autistic. Kuma an ce an yi masa ganin ƙarshe lokacin da ya bar gida da misalin ƙarfe 4 na yamma a Zariya.

Ya dai musanta raɗe-raɗin cewa an ƙwaƙwale idanuwan yaron, amma dai ya shakka akwai jini a kafar idanuwan.

ASP Mansur Hassan ya ce daga bayanan da suka samu yaron sun je Zariya ne ziyara daga Kano kafin wannan ƙaddara ta faru da shi.

A cewarsa, sun baza koma domin samun bayanan da za su taimaka musu ga kama mutanen da suka tafka wannan aika-aika.

Ya dai ce zuwa yanzu ba su kai ga kama kowa ba, sai dai tuni suka miƙa gawar Ibrahim Mohammed ga iyayensa domin yi masa sutura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *