Ƴan sanda sun kama matar da ta ajiye zaki a gidanta

Spread the love

Yan sanda a kasar Thailand sun kama wata mata da aka dauki hoton zakin da ta mallaka ta ajiye a gidanta yana yawo a cikin mota a titunan Pattaya.

Bidiyon da a yanzu ya fara yaɗuwa ya nuna ɗan zaki mai ɗaure a sarka yana zaune a bayan wani farin mota.

Wani dan kasar Sri Lanka ne ke tuƙa zakin wanda a hanlin yanzu ya bar kasar, kuma ana kyautata zaton abokin matar mai zakin ne, Sawangjit Kosoongnern.

Duk da cewa mallakar zaki a Thailand ba bisa ka’ida bane, hakan na buƙatar a yi masa rajista a hukumance.

Hukumomi a Thailand sun ce Sawangjit ta yi ikirarin cewa ta sayi dabbar daga hannun wani dan ƙasar Thailand a lardin Nakhon Pathom, wanda ya yi nasarar kai zakin zuwa Pattaya.

Sai dai ya gaza wajen samun jami’ai su duba kafin ya siyar da zakin, lamarin da ya sanya mallakar dabbar haramtacciya.

Don haka tana fuskantar tuhumar mallakar dabbar dawa ba tare da izini ba, wanda ke da hukuncin daurin shekara guda a gidan yari da tarar baht 100,000 kwatankwacin dalar Amurka 2,800 kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *