Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 16 da ake zargi da aikata miyagun laifuka da kuma garkuwa da mutane a Abuja, babban birnin ƙasar.
Hakan ya biyo bayan kaddamar da rundunar ‘yan sanda ta musamman da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, ya yi kwanan nan, inda har suka samu nasarar kama mutanen da kwato makamai da alburusai a babban birnin tarayya Abuja.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan ta Najeriya, Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce rundunar haɗin gwiwa ta jami’ansu sun kuma kama wasu mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
Daga cikin waɗanda aka kama a ranar Asabar ɗin, akwai wasu masu garkuwa da mutane uku, waɗanda kuma ake zargi da aikata fashi da makami a karamar hukumar Bwari da sauran sassan Abuja.
“Daga cikin nasarorin da aka samu akwai yadda aka dakile wani shirin yin garkuwa da mutane ta hanyar leken asiri wanda ya yi sanadin kama masu garkuwa da mutane a Bwari, da kwato makamai daga hannunsu,” in ji sanarwar.
Haka-zalika, ƴan sandan sun cafke wani mai sayar da bindigogi mai suna Everest Magaji, a lokacin da yake tattaunawa da wasu gungun ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a yanzu, domin sayar musu da muggan makamai da alburusai.
Sun ce sun kwato bindiga kirar pistol guda 11, da kuma ta harbi ka ruga biyu daga hannun wanda ake zargin.