Ƴan sanda sun kama wani matashi kan zargin kashe yayansa a Bauchi

Spread the love

Rundunar ƴan sanda jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Isyaku Babale, bisa zargin  daɓa wa yayansa wuka har lahira.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Ahmed Wakili ya fitar, ta ce binciken farko da suka gudanar, ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wuka wajen daɓa wa babban wansa mai suna Abubakar Balewa ranar Lahai, 31 ga watan Maris bayan cacar-baki da ta ɓarke tsakaninsu.

Wakili ya ce bayan samun rahoton abin da ya faru ne, sai suka tura jami’ansu zuwa wurin, abin da ya kuma ya kai ga kama matashin mai shekara 30 wanda ke zaune a Anguwan Dawaki.

Ya ce bayan garzayawa da mutumin asibiti ne likita ya tabbatar da cewa ya mutu.

Binciken da aka gudanar ya ƙara nuna cewa ƴan uwan junan sun saba yin faɗa da juna ta hanyar amfani da muggan makamai, sai dai, a wannan karo, har ta kai ga rasa ran ɗaya daga cikinsu.

“Cacar-baki tsakanin ƴan uwan ta ɓarke ne bayan da wanda ake zargin ya faɗa wa ɗan uwansa da ya kashe da ya daina shan ‘Sholi’ a ɗakinsu saboda warinsa, wannan abin ne ya janyo faɗa tsakaninsu.

“Jim kaɗan bayan an shiga tsakaninsu ne, wanda ake zargin ya ruga ya ɗauko wani abu da ake kyautata zaton wuƙa sannan ya daɓa wa yayan nasa a ciki,” in ji Wakili.

Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, suka shiga farautar wanda ake zargin inda har ta kai ga kama shi a Kasuwan Shanu na jihar ta Bauchi.

Wakili ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Auwal Mohammed, ya bayar da umarnin yin cikakken bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *