Ƴan sandan Najeriya sun kama wani babban ɗan Kirifto

Spread the love

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan wani babban ɗankasuwar Kirifto da aka fi sani da sunan Blord da ta kama.

Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kama Blord ne kan zargin damfara ta hanyar amfani da kirifto.

A sanarwar, rundunar ta ce tana bincike bayan koke da ƙorafi da ta samu game da kamfanoni da suka hada da na gidaje da ake fakewa da kirifto da ke da alaƙa da wanda take zargi Blord.

“Lifukan sun haɗa da zargin damfara da sunan kirifto, da damfara a intanet da laifukan damfara na kwamfuta da tallafi ga ta’addanci,” a cewar sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *