Jami’an tsaro a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta-da-kayar-baya a yankin Achalla da ke karamar hukumar Awka ta arewa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga ya fitar, ya ce sun kwato motoci biyar da miyagun makamai da suka gano a maoyar ‘yan ta’addan.
Ikenga ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kawo cikas a kasuwar Achalla a ranar Litinin ɗin da ta gabata, lamarin da ya tilasta wa ‘yan kasuwar su zauna a gida.
”Hakan ya jawo hankalin jami’an tsaro a jihar wanda hakan ya sanya rundunar ‘yan sandan jihar ta yanke shawarar maida masu martani da sanyin safiyar ranar Litinin,” in ji Ikenga.
Yawan marasa aikin yi ya ƙaru a Najeriya bayan cire tallafin man fetur
Ecowas na tunanin yadda za a sassanta da Nijar da Mali da Burkina Faso
Ya ce sakamakon nasarar da aka samu ya kai ga kwato wasu manyan motoci guda biyar da aka kwace a baya.
Haka kuma an samu harsashin bindiga sama da 300 na bindigar Ak-47.”
Dukkan ma’aikatan da suka fito daga ayyuka daban-daban sun koma sansaninsu lafiya, a cewar kakakin ƴan sandan.