Ƴan sandan Najeriya za su fara amfani da fasahar zamani wajen rijistar motoci

Spread the love

Rundunar ƴan sandan Najeriya za ta fara amfani da fasahar zamani wajen rijistar motoci a ƙasar nan da kwana 14.

Rundunar ta ce daga ranar 29 ga watan Yulin 2024, sabon tsarin mai amfani da na’urorin zamani, zai fara aiki domin inganta tsaro a sassan ƙasar.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi a cikin wata sanarwa ya ce tsarin wanda aka yi wa laƙabi da e-CMR zai taimaka wajen inganta aikin jami’an ƴan sanda wajen gudanar da bincike da daƙile aikata laifuka ta amfani da ababen hawa, har ma da ayyukan ƴan bindiga da masu tayar da ƙayar baya.

Sanarwar ta ce sabon tsarin rijistar ababen hawan zai riƙa amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan kai tsaye na ababen hawa da waɗanda suka mallake su da kuma ayyukan da suke yi da su.

Hakan na nufin daga lokacin fara aiki da wanna sabon tsari, duk wasu sauye-sauye na takardun mota ko kuma wasu sassan motar za su gudana cikin sauki ba kamar yadda a baya ake ɗaukar lokacin haɗa irin waɗannan takardu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *