Ƴansanda sun fara bincike kan gawar namiji sanye da kayan mata da aka tsinta a Abuja

Spread the love

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta fara gudanar da bincike kan sanadin mutuwar, wani mutum da aka ga gawarsa, sanye da kayan mata a Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce, a yau Alhamis ne 8 ga watan Agusta, 2024, da misalin 07:40 na safe, aka sanar da rundunar ta waya cewa an ga wata mata da ba a sani ba kwance ba ta motsi a titin Katampe – Mabushi, inda nan da nan aka tura ƙwararrun masu bincike zuwa wajen.

Sanarwar ta ce, binciken farko-farko ya nuna cewa namiji ne sanye da kayan mata, kuma babu wata alama da za ta nuna ko wane ne shi.

Ta kara da cewa daga nan ne aka tafi da shi asibitin Gundumar Maitama (Maitama District Hospital), inda likitoci suka tabbatar ya rasu.

Sanarwar ta ce, nan da nan kwamishinan ‘yansandan Abuja, CP Benneth C. Igweh, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan sanadin mutuwar mutumin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *