Ƴansanda sun jefa wa masu zanga-zanga hayaƙi mai sa hawaye a Senegal

Spread the love

Jami’an tsaro a Senegal sun jefa wa masu zanga-zanga a ƙofar Majalisar dokokin ƙasar hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa mutanen da suka taru domin nuna adawa da ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka tsara yi ranar 25 ga wannan wata.

Magoya bayan jam’iyyun adawa sun yi aniyar gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ce a gaban ginin majalisar dokokin, sai dai jami’an ƴansanda sun tarwatsa su tare da kama wasu.

Hakan ya faru ne jim kaɗan gabanin fara muhawara a zauren majalisar game da ƙudurin ɗage zaɓen shugaban ƙasar zuwa ranar 25 ga watan Agustan 2024.

Kamfanin dillancin labaru na AFP  ya ruwaito wasu daga cikin masu zanga-zangar na furta kalaman “Macky Sall ɗan kama-karya” yayin da aka tarwatsa su.

Ƴan takara na jam’iyyun hamayya sun yi tir da matakin ɗage lokacin zaɓen, inda suka bayyana shi a matsayin ‘juyin mulki ga kundin tsarin mulkin ƙasar.’

Sannan sun yi kira da a gudanar da zanag-zanga a faɗin ƙasar kuma a tabbatar an yi zaɓen a lokacin da aka tsara tun da farko.

An dai katse sadarwar waya da intanet sannan an dakatar da wani gidan talabijin mai zaman kansa.

Senegal ta shiga hali na tangal-tangal tun bayan da shugaban ƙasar Macky Sall a ranar Asabar ya sanar da cewa za a ɗage yin zaɓen ƙasar, awanni kaɗan kafin fara yaƙin neman zaɓe a hukumance, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *