Ƴansanda sun kama matar da ake zargi da kashe mijinta a Abuja

Spread the love

Rundunar ƴansandan Abuja babban birnin Najeriya ta sanar da kama wata mata bisa zarginta da hannu a kashe mijinta.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce dakarunta sun kama Rahimat Salaum ne a lokacin da take ƙokarin tserewa da wasu kayan maigidan nata bayan an kwashe kwanaki uku ana neman ta.

Sanarwar ta ƙara da cewa wadda ake zargin ta tabbatar da kashe mijin nata bayan rikici ya kaure tsakaninsu, kuma daga baya ta kai jami’an wani kango inda ta ɓoye gawar da ke da alamun ƙuna a jikinta.

Rundunar ta ce ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

“Kwamishinan Ƴansandan Abuja CP Benneth C. Igwe ya bayar da tabbacin cewa za a ɗauki matakan da suka dace wurin tabbatar da an yi hukuncin da yakamata,” in ji sanarwar. facebook , idongari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *