Rundunar ƴansandan jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ƴansandan jihar Ibrahim Adamu Bakori ta ƙwato tare da miƙa kuɗi naira 4,850,000 ga mutumin da aka yi garkuwa da shi, bayan ƴansandan sun ceto shi, tare da ƙwato kuɗin daga hannun masu garkuwa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce ƴanbindigar sun yi garkuwa da mutumin a garin Zakirai da ke ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano, sannan da farko suka buƙaci suka buƙaci kuɗin fansa naira miliyan 15.
“Da muka samu labari, sai jami’anmu suka ƙaddamar da farautar ƴanbindigar, inda suka kama waɗanda ake zargi guda biyar, sannan aka ceto mutumin a ranar 17 ga watan Maris.”
Sanarwar ta ƙara da cewa an mayar da kuɗin ne ta hannun shugaban ƙaramar hukumar Gabasawa, Sagir Usman Abubakar, wanda ya yi godiya a madadin mutumin da al’ummar mutanen yankin.
A ƙarshe kwamishinan ƴansandan ya buƙaci mutanen jihar su zama masu sa ido, tare da kai bayanin duk wani abu da suke zargi ko ya ɗaure musu kai.