Ƴar damben Najeriya ta gaza tsallake gwajin shan ƙwayar ƙara kuzari a Olympics

Spread the love

An dakatar da yar wasan damben Najeriya, Cynthia Ogunsemilor daga gasar Olympics bayan da ta gaza tsallake gwajin shan ƙwayar ƙara kuzari.

Gwajin da aka yi wa Ogunsemilor, wadda ta samu lambar yabo ta zinare a wasan Africa Games a birnin Accra a farkon shekarar nan da kuma tagulla a gasar commonwealth a Birmingham, ya nuna tana shan furosemide, ƙwayar da aka haramta sha.

Hukumar da ke bincike kan amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari tsakanin ƴan wasan motsa jiki ce ta yi gwajin a ranar 25 ga watan Yuli a madadin kwamitin shirya gasar Olympics.

Ƴar wasan mai shekara 22 na da damar ƙalubalantar sakamakon sai dai duk wani mataki ba zai zo kan lokaci ba a abin da ka iya zama farkon wasanta a gasar Olympics a karawarta da Shih Yi Wu ta China a ranar Litinin na ajin masu nauyin kilo 60.

Sakamakon Ogunsemilor na nufin yanzu Najeriya tana da ƴan wasan da aka dakatar saboda karya dokokin da suka shafi shan ƙwayoyin ƙara kuzari a wasan Olympics biyu jere bayan Blessing Okagbare da aka dakatar shekara uku da ta gabata a Tokyo.

Daga bisani an dakatar da Okagbare tsawon shekara 11 saboda amfani da wani sinadarin ƙara kuzari.

Akwai fargabar da ake cewa ba lalle bane a ƙyale yan wasan Najeriya su yi wasa a ƙarƙashin tutarsu saboda zarge-zargen hukumar da ke yaƙi da shan ƙwaya a wasanni cewa irin wannan hukumar da ke ƙasar ba ta mutunta dokokinta.

Kwamitin yaƙi da shan ƙwaya a wasanni na Najeriya ya musanta zarge-zargen kuma kotun sauraron ƙararrakin wasanni na kan bincike

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *