Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya.
Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse.
Ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Yusif Bashir da motar asibiti ƙirar Toyota Land Cruiser mai lambar ONG-0777, bayan ya shigo da ita ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar.
- Ana Tuhumar Dan Nijeriya Da Budurwarsa Da Zargin Kisan Kai A Kasar Zambia
- Yan Sanda Sun Dakatar Da Kama Motoci Masu Duhun Gilasai
Tahir, ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen miƙa sh ga rundunar ’yan sandan jihar, domin ci gaba da bincike.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.