Ɓata-gari ka iya mafani da katsewar Intanet don aikata laifuka – Masana

Spread the love

Masana harkar tsaron intanet sun yi gargaɗin cewa ɓata-gari ka iya amfani da matsalar katsewar intanet don aikata miyagun laifuka.

A yau ne hukumar Kula da tsaron intanet ta Australiya (ASD), ta fitar da sanarwar game da masu satar bayanai da ke aika saƙonnin iƙirarin yin gyare-gyaren manhajojin daga kamfanin ‘CrowdStrike’, mai kula da tsaron intanet.

“Gargaɗi! Mun fahimci yawancin shafukan intanet marasa kyau da masu fitar da lambobin da ba na hukuma ba suna iƙirarin taimakawa ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi don warware matsalar katsewar intanet da aka fuskanta” in ji sanarwar.

Don haka hukumar ta yi kira ga masu amfani da fasahar intanet, da su yi amfani da manhajar kamafanin ‘CrowdStrike’ kawai don samo bayanai da duk wani taimako da suke buƙata.

Gargaɗin ASD na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da Cibiyar Tsaron Intanet ta Burtaniya (NCSC) ta yi a jiya don mutane su yi taka-tsan-tsan da sahihancin saƙon imel ko kuma kiran da ke nuna cewa na CrowdStrike ne ko taimakon Microsoft.

Tun a jiya ne dai aka fuskanci katsewar intanet ɗin a wasu sassan duniya, lamarin da ya haifar da tsaikon abubuwa da dama ciki har da tashin jirage da katsewar wasu kafofin yaɗa labarai da aiki a wasu asibiton faɗin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *