Wani ɗalibi mai suna Ogbeche, ya kashe malaminsa Oshen, a makarantar sakandire da ke garin Ugboro, a Ƙaramar Hukumar Bekwarra a Jihar Kuros Riba.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya yi ƙoƙarin raba faɗa tsakanin Ogbeche da wani ɗalibi.
Sai dai a fusace, ɗalibin ya fisge taɓarya daga hannun wata mata, ya buga wa malamin a kai, wanda hakan ya sa ya faɗi sumamme.
Duk da garzayawa da shi da aka yi zuwa asibiti, likitoci sun tabbatar da mutuwarsa.
- Yan Sanda Sun Cafke Dillalan Tabar Wiwi 11 A Abuja
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Kwayoyi Na Sama Da Naira Miliyan 80
Wata ganau mai suna Lizzy ta ce: “Malamin kawai yaje rabon faɗa ne, amma Ogbeche ya fusata ya ɗauki taɓarya ya buga masa a kai, nan take ya faɗi.”
Al’ummar yankin sun nuna ɓacin ransu, inda suka ce abin da ɗalibin ya aikata ba abin yadda ba ne, domin ya hallaka malaminsa.
Yanzu haka, rundunar ’yan sandan jihar, ta kama Ogbeche, inda ake masa tambayoyi kafin a miƙa shi zuwa hedikwatar rundunar domin ci gaba da bincike.