Ɗan sanda ya harbe alƙali ana tsaka da shari’ a kotu

Spread the love

Wani babban jami’in ‘yan sandan Kenya ya harbi mai jagorantar shari’a a wata kotun majistare da ke Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.

Dan sandan mai muƙamin babban Isfekta ya buɗe wa mai shari’a Monica Kivuti wuta jim kaɗan bayan ta yanke wa matarsa hukunci kan wani laifi da ake zarginta da aikatawa.

Rahotonni sun ce jami’in ɗan sandan ya fusata ne bayan da kotun ta ƙi amincewa da buƙatar belin matar tasa.

Daga nan ne, Sufeto Samson Kipchirchir Kipruto – wanda ke jagorantar ofishin ‘yan sanda na Londiani da ke yammacin ƙasar – ya zaro bindigarsa tare da harbe alƙaliyar inda ya ji mata rauni.

Nan take kuma jami’an ‘yansanda da ke kotun suka mayar da martani, inda ɗaya daga cikinsu ya harbe tare da kashe mista Kipruto.

Rahoton ‘yan sanda ya nuna cewa uku daga cikin jami’an tsaron da suka mayar da martanin sun samu raunuka a musayar wutar da suka yi da mista Kipruto.

Tuni dai aka garzaya da alƙaliyar da sauran jami’an ‘yan sandan uku zuwa asibiti domin yi musu magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *