Ɗan Sanda Ya Mutu A Cikin Jirgin Ƙasan Abuja Zuwa Kaduna

Spread the love

Ɗaya daga cikin jami’an ’yan sandan da ke bayar da kariya a cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rasu ana tsaka da tafiya.

Wani fasinja da ke cikin jirgin, ya ce lokacin da jirgin kasan ya tashi daga Kaduna babu wata alamar rashin lafiya a tattare da marigayin

Fasinjan, ya ce daga baya ɗan sandan ya bayyana cewar kirjinsa na masa ciwo, inda ya nemi taimako kafin daga bisani rai ya yi halinsa.

“Wani ɗan sanda, wanda yana ɗaya daga cikin masu rakiyar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya mutu. Ya bar gida cikin ƙoshin lafiya.

“Amma ana tsaka da tafiya, sai ya ce kirjinsa na masa ciwo, ya kuma nemi abokin aikinsa ya kawo masa magani.

“Babu likitan da zai ba shi agajin gaggawa a cikin jirgin. Wani fasinja wanda likita ne a cikin jirgin ya yi ƙoƙarin ba shi agaji, amma jami’in ya riga ya rasu,” in ji fasinjan.

Bayan ɗan sandan ya rasu, an ajiye gawarsa a wani sashe na jirgin, inda aka rufe fuskarsa.

Bayan rasuwar ɗan sandan, fasinjojin da ke cikin jirgin sun taru, inda suka dinga tattaunawa kan faruwar lamarin.

Jirgin ƙasan ya isa tashar Kubwa da ke Abuja da misalin ƙarfe 3:20, inda ya sauke wasu fasinjoji.

Jami’an tsaro da ke cikin jirgin ƙasan, sun hana mutane ɗaukar hoton jami’in.

Bayan tsayawar jirgin a tashar Kubwa, wasu motocin ‘yan sanda sun shiga tashar domin ɗaukar gawar zuwa ɗakin ajiyar gawa.

Ƙokarin jin ta bakin kakakin Kamfanin Jiragen Ƙasa na Najeriya, Mahmoud Yakubu, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *