Ɗaukar matakan shari’a da gangan ne ke ɓata sha’anin jagoranci a PDP’

Spread the love

Majalisar Amintattu ta jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa akwai wasu mambobin jam’iyyar da ke yi wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar zagon ƙasa ta hanyar ɗaukar matakan shari’a ga shugaba da sakataren jam’iyyar.

Shugaban kwmaitin, Sanata Adolphus Wabara ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron majalisar gudanarwar jam’iyyar da ake yi a Abuja.

Sanata Wabara ya ƙara da cewa ɗya daga cikin abubuwan da ke damun ‘yan jam’iyyar shi ne ” halin da shugabancin jam’iyyar ke ciki a yanzu haka.”

Batun jagorancin jam’iyyar ne dai yake kokarin raba kan jama’a, inda ko a ranar Laraba sai da wani ɓangare na ‘yan jam’iyyar suka gudanar da zanga-zanga a sakatariyar jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *