Wakilin Kananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar Wakilai ta kasa, RT. Hon Kabiru Alhassan Rurum ya bukaci iyaye da su rinka kyale ‘ya’yansu mata Musulmi shiga aikin Soja domin Akwai bukatar su, a cikin aikin kuma suna da rawar da za su taka..
RT Hon Kabiru Rurum ya yi wannan kira a Yau lokacin daya Karbi bakuncin iyalan Alhaji Adda’u Isa Rano, da suka ziyarce shi a ofishinsa na Kano don yi masa godiya bisa shigewarsa gaba wajen Samarwa Hindatu Adda’u Isa aikin sojin Saman a rundunar Sojin Saman Najeriya.
Ya ce akwai bukatar ci gaba da ba wa mata kwarin gwiwar shiga dukkanin aikin damara domin Akwai gudummuwar da zabsu bayar ga aikin ta fuskar addini da Harshe da Al’adunsu dama Ci gaban kasa.
Da yake jawabi tunda Farko jagoran tawagar Alhaji Dahiru Adda’u Isa ya ce zuri’ar ta Alhaji Adda’u za su ci gaba da Alfahari da yin Addu’oin daukaka ga Hon Kabiru Alhassan Rurum din bisa yadda ya tsaya tsayin daka har kanwar tasu ta samu Cimma burinta na rayuwa ta Kuma zama mace ta farko daga yankin Kano ta Kudu da ta shiga aikin sojin sama Wanda tarihi ba zai manta da ita ba.
Sun Kuma yi Addu’a ga iyaye da magabatan Turakin na Rano da fatan Ayyukan Alkhairin da yakeyi ga Al’umma Allah ya isar gare su.
*Fatihu Yusuf Bichi*
*Media Aide to Rurum*
*Member Representing Rano, Kibiya & Bunkure Federal Constituency, Abuja*
*Nov 3rd, 2024.