Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ake Zargi Da Tarwatsa Farin Cikin Wasu Ma’aurata A Kano

Spread the love

 

Rundunar yan Sandan jahar Kano, ta kama Wani matashi Mai suna, Amir Muhd Dan Shekaru 23, mazaunin unguwar Sharada, bisa Zargin sa da Yi wa wasu ma’aurata raunuka da wuka , a lokacin da suke bacci a gidansu.

Tun a ranar 28 ga watan Oktoba 2024 , aka shigar da korafi, a ofishin Yan Sanda da cewar Wani ya shiga gidan mutumin tare da yankarsa a sassan jikinsa kuma ya fadi cikin Jini.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bayan samun korafin kwamishinan yan Sandan jahar, CP Salman Dogo Garba, ya sa aka garzaya da shi babban asibitin Kwararru na Murtala Muhammed Kano, Inda aka samu yankan wuka masu yawa a sassan jikinsa.

Haka zalika an samu raunuka a jikin matarsa, da Ake Zargin matashin da Yi musu raunuka.

 

Binciken Farko- farko ya tabbatar da cewa Wanda Ake Zargin ya amsa laifinsa da cewa shi ne ya shiga gidan da niyar satar waya, Amma ya Yi amfani da wukar ya yanyanke mu su.

Anasa bangaren magidancin ya bayyana farin cikinsa da kuma godiya ga rundunar Yan Sandan Kano, bisa nasarar da suka samu wajen cafke Wanda Ake Zargin.

” Ya Yi mun yanka goma sha daya , ita kuma matata na Yi mata yanka guda 5″ cewar Magidancin “.

A karshe SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an dawo da Amir Muhd, babban sashin gudanar da binciken manyan laifuka, don fadada bincike kuma da zarar an kammala za a Gurfanar da shi a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *