Gwamnatin jihar Kebbi ta jajanta wa al’ummar Waje da ke karamar hukumar Danko Wasagu sakamakon harin ‘yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar manoma 15 tare da jikkata wasu 3.
Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya mika sakon ta’aziyyar gwamnati tare da bayar da tallafin Naira miliyan 24 ga iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.
Ya bayyana hakan a matsayin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a wannan lokaci mai cike da kalubale.
Sanata Abubakar, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace don magance matsalar rashin tsaro, tare da baiwa manoma damar gudanar da ayyukansu cikin aminci.
- Tsantsar Talauci Ne Ya Haifar Da Matsalar Tsaro : Gwamna Uba Sani
- An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja
Shugaban karamar hukumar Danko Wasagu, Alhaji Hussaini Aliyu Bena, ya tabbatar da cewa an kashe manoma 15 tare da jikkata wasu 3 a harin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai.
Hakimin Waje, Alhaji Bala Danbaba, a lokacin da ya yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan ziyarar da kuma tallafin kudi, ya bayyana cewa, iyakar Danko Wasagu da jihohin Neja, Zamfara da kuma Sokoto na haifar da matsala, inda ya yi kira da a kara inganta tsaro domin toshe wadannan hanyoyin shiga.