Hukumar Hisbah a Kano ta fara kama matuka baburan adaidaita Sahu dake Askin banza, sanya gajerun wanduna da kure sautin kida.

Spread the love

 

Kimanin matuka Baburan a dai daita sahu guda 100 Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta yi holinsu a shalkwatanta da ke unguwar Sharada, wadan da suka taka dokar sana’ar daukan fasinja da ta aikin a kwaryar birnin kano.

Da yake karin haske a kan matuka Baburan a dai daita sahun, Babban kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce daga cikin an sami mutane 24 da laifin cakuda maza da mata a baburansu, sai mutane 35 wadan da suka yi Askin banza, mutum 12 sun lika hotunan batsa a jikin baburansu, da wadan da ke sanye da gajirun waduna mutum 11 da masu kure sautin kida ya yin tuki da sauransu

Hukumar Hisbah a Kano ta cafke Ramlat Princess bayan ta tallata kanta a fanfen bidiyo cewar duk namijin da zai aure ta sai ya kawo macen da za su yi latata.

Wani Sojan Baka da ake zargi da laifin yin Sojan Gona da sunan Arewa Radio Kano da karbar kudaden wata mata ya shigar da gidan radio, yan sanda da wasu mutane 9 kara kotu ta hana kama shi.

Babban kwamandan Hisbah wanda ya yi magana ta hannun mataimkinsa mai kulla da aiyukan yau da kullum (operations) Dr. Mujahid Aminudeen Abubakar, ya ce daga yanzu Dakarunsa zasu ci gaba da sa ido domin tsaftace sana’ar a dai daita sahun a jihar kano.

Babban kwamandan hukumar Hisbah yace babban abin takaici, mafirinjaye daga cikin adadin wadan da Dakarunsa suka kamo, ko da aka bukace su da gabatar da rukunan sallah ba su iya ba, daga cikin har da wadan da su ka kasa karanta Fatiha da sura dai.

Ya kara da shawartan iyaye da sauran jama’a da su dage wajen sauke nauyin da shariya ta yi ummarci uba ko uwa ya yi Musaman a kan neman illimin addini da na zamani, dan samar da al’uma mai cike da tarbiya da kyawawan aiki a rayuwa.

A karshe ya ba da ummarnin ga sashin wayar da kai da na Da’awa da su koyawa wadan da su ka kasa karanta Fatiha da sura da wadan da su ka gaza kawo rukunan sallah har sai sun iya a matsayin beli, tare da daukan cikakken suna da addireshi da lambar a dai daita sahun.

A nata jawabin mataimakiyar babbar kwamandan Hisbah Mai kulla da sashin mata, Dr. Khadija Sagir Sulaiman ta shawarci masu sana”ar tuka Baburan a dai daita sahun a jihar kano da su Ji tsoron Allah kuma su dai na cakuda maza da mata a baburansu domin samun daukaka da arziki a sana’ar.

Babban jami’in Hisbah Mai kulla da sashin aiyukan yau da kullum, ACG Abubakar Salihu yace Dakarunsa sun gabatar da sumame da cafke matuka Baburan a dai daita sahun a kan titin gidan murtala/ BuK, da titin Kofar kabuga/ Kofar Ruwa, kabuga/titin tal’udu/ zuwa Asibitin murtala, da titin gidan sarki/ Kofar Nassarawa dasauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *