Hukumar ilimin bai daya ta jahar Kano za ta hukunta malaman makarantar da basa zuwa wajen aiki: Malam Yusuf Kabir

Spread the love

Shugaban hukumar Ilimin bai daya na jahar Kano, Malam Yusif Kabir , ya nuna damuwarsa bisa halayyar da wasu daga cikin malaman makaranta ke nuna wa, takin zuwa wararen aiki.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gana wa da sashen yada labarai na hukumar ilimin bai dayan a ranar Alhamis.

Malam Yusuf , ya kara da cewa daidai lokacin da gwamnatin jahar Kano ta fito da managartan tsare-tsare na inganta harkokin ilimi ta hanyar inganta rayuwar malaman, musamman wajen biyan su albashi akan lokaci da kuma sanya mu su kudin Karin girma,sai dai marasa kishi daga cikinsu na ci gaba da kin zuwa wuraren aikinsu na koyarwa.

Tinubu ya koka kan yadda ake yi wa yan Najeriya kuɗin-goro kan miyagun laifuka

Kano: Kotu ta bayar da belin Danbilki Kwamanda

Idongari.ng, ya ruwaito cewa , hukumar ta inganta fannin duba makarantu don samun cikakken bayanin abubuwa da suke wakana a makarantu da nufin daukar matakin da ya dace.

Ya kuma ja hankalin wadanda suke da irin halayyar ta kin zuwa aiki , su sauya hali tun kafin hukumar ta dauki matakin ladabtarwa a kansu.

Malam Yusuf , ya godewa gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, bisa bayar da fifiko ga fannin ilimi, inda ya bukaci al’ummar jahar da su kara bai wa gwamnatin goyon baya a kokarinta na inganta harkokin ilimi da sauran al’amura da suka shafi ci gaban jahar baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *