Yan sandan Kano sun cafke kasurgumin mai garkuwa da mutane, satar shanu, da suka addabi Birnin Gwari,Katsina, Zamfara.

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi mai  Isa Lawal mai shekaru 33, da ake zargin ya kware wajen yin garkuwa da mutane, satar shanu da kuma fashi da makami a yankin Birnin Gwari a jahar Kaduna.

Rundunar yan sandan ta samu nasarar kama matashin a karamar hukumar Karaye ta jahar Kano, a lokacin da jami’an yan sandan da suke yaki da masu garkuwa da mutane suke gudanar da aiyukansu karkashin jagorancin SP Aliyu Mohammed Auwal, inda aka samu shanun sata 55 da kuma Tumaki 6.

Mukaddashin mai Magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano, ASP Abdullahi Hussaini, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a yau Litinin.

Sanarwar ta ce, a ranar 4 ga watan Fabrairu 2024 da misalin karfe 5:40pm , jami’an suka cafke Isa Lawal, mazaunin Garin Kaya dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Aiki ya samu Atiku Abubakar – Fadar shugaban Najeriya

Yadda mazauna birnin Minna ke zanga-zangar tsadar rayuwa

ASP Abdullahi Hussaini ,ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa, da cewar ya gudo ne daga sansanin ‘yan bindigar Maidaro ta karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna bayan sun yi artabu da yan bindigar da ke karkashin jagorancin Boderi Isiya wadanda suke a cikin Daji .

Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya bayyana sunan shugaban kungiyar su mai suna Bashir Malumfashi ta jahar Katsina, wanda aka kashe, a artabun da bangarorin biyu suka yi, shi yasa yabar maboyarsu ta Birnin Gwari, domin kafa sabon sansani a yankin Gwaro da Karaye dake jahar Kano.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhmmed Usaini Gumel,ya yaba da kokarin jami’an kan yadda suke gudanar da aiyukansu, tare da bada tabbacin kara jami’an tsaron akan iyokokin jahar don ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Wanda ake zargin ya tabbatar da cewa, sune suka addabi mutanen jahohin Kaduna, Katsina da kuma Zamfara, wajen yin garkuwa da jama’a don karbar kudin fansa , tare shugaban su Mu’azu Mai Bokolo ya tsere da bindiga kirar AK47 guda uku.

Kwamishinan yan sandan Kano CP Muhammed Gumel, ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike domin cafke sauran wadanda ake zargin da hana al’umma sakat don su fuskanci hukunci.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *