Yan Kasuwa a Kano Sun Koka Kan Kama Kayansu da Hukumar Kwastom Keyi

Spread the love

Yan Kasuwar da ke gudanar harkokin kasuwanci a jihar Kano na ci gaba da kokawa bisa kama Kayansu da Hukumar Kwastom Keyi ba tare da wani dalili ba.

Na kamu da cutar tsananin damuwa bayan rabuwa da matata :Zango

Yan kasuwar sun ce jami’an na Kwastom na matsa mu su ta hanyar Kafa shigen bincike Masu yawan gaske a manyan Hanyoyin Fita na Jihar Kano, Musamman Titin Maiduguri da hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Kamal Yahya Matashin dan kasuwa ne Dake Fitar da Kaya daga Jihar Kano zuwa wasu jihohi ya Bayyana wa Idongari.ng cewa  jami’an Kwastom Suna kama motocin Yan Kasuwa.

Dan Kasuwar ya Bayyana cewa jami’an sun yi ikirarin Harbin direban da yake daukar masa Kaya tare da zargin kwace masa motoci da Kayan da yake kasuwanci guda 8 wanda Ya Bayyana cewa Kayan basa cikin jerin Kayan da Hukumar Hana Fasakauri ta Kwastom ta haramta shigo dasu ko Fita dasu.

Shugabannin kananan hukumomi uku sun fice daga APC zuwa NNPP mai mulkin Kano

Rundunar yan sandan Kano ta shirya tsaf don bayar da cikakken tsaro a ziyarar Uwar gidan shugaban kasa Oluremi Tinubu.

Wani direba Dake dakon Kayan Yan kasuwan da yanemi a sakaye sunansa ya Bayyana wa , idongari.ng cewa jami’an Kwastom na matsa musu da karbe karben kudaden cin Hanci a hannunsu wanda suke kira da D O Inda ya ce jami’an sukan karbi naira dubu biyar zuwa dubu goma ga duk motor da suka tare. A Karshe Kamal Yahya ya yi kira da Gwamnatin Jihar Kano Karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta shiga lamarin don gudun tabarbarewar Harkar kasuwanci.

Duk kokarinmu na jin tabakin Hukumar Hana Fasakauri shiyar Kano da Jigawa don jin suna sane da Wannan zargi da Yan Kasuwa ke musu bamu samu damar Hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *