Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

Spread the love

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta tisa keyar jarumar TikTok Ramlat Mohammed zuwa gidan yari kan zargin badala da karuwanci.

A ranar Juma’a ne Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa na kotun Musuluncin da ke unguwar Sharada ya sa ajiye Ramlat a gidan yari bayan Hukumar Hisbah ta gurfanar da ita.

A kwanakin nan ne wani bidiyon Ramlat ta ya karade shafukan sada zumunta, wanda a ciki take tallata madigo, har ta bayyana kanta a matsayin mai wannan muguwar dabi’ar.

A cikin bidiyon, an ji matashiyar na cewa, duk wanda ai aure ta, to dole sai ya amince cewa ita za ta auro tata matar, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Takardar karar ta bayyana cewa an sami jarumar Tiktok din tana yin amfani da kafar sada zumunta tana yin kalaman badala.

A cewar takardar kara laifukan da ake zargin ta da su laifuka ne da suka saba da sashe na 341 da 275 da 227 na Kundin Penel code.

Wacce ake zargin ta amsa laifukan inda ta nemi afuwar kotu bisa laifukan da ta aikata.

Sai dai saboda kurewar lokaci kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 19 ga Fabrairu don yanke hukunci.

Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace ɗaliban Ekiti

An karrama yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba

Haka kuma kotun ta yi umarnin tisa keyar Ramla zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a sake dawowa gaban kotun.

Wannan na zuwa ne bayan wata kotun Musulinci a jihar ta yanke hukuncin daurin wata shida kan laifin badala ga wani mai suna Murtala Adamu, wanda aka kama tare da fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.

Kotun da ke unguwar Gama ta bai wa matashin zabin biyan tarar N30,000 kan laifin tayar da haniya da aikata badala.

An yanke masa hukuncin ne washegarin da kotun ta sa a tsare Murja a gidan yari kan laifin badada da koyar da karuwanci.

An gurfanar da Murja ne bayan an kama su da Murtala Adamu a unguwar Hotoro, bayan jami’an Hukumar Hisbah Kano, sun kai samame sakamakon korafin da mazaunar unguwar suka shigar.

Murja dai ta musanta zargin da ake mata na koyar da karuwanci, badala, da kuma tayar da hankali jama’a.

Kotun dai ta yanke alakar Murtala da Murja Kunya da cewa ba shi ba ita, sannan ta haramta masa zuwa unguwar tsawon shekaru biyu, kuma muddin aka gan shi zai dandana kudarsa.

Daily Trust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *